Yayin da mahara ke ci gaba da cin karfin kai samame a cikin kauyukan Jihar Zamfara, Gwamna Bello Matawalle zai gaba da masana kuma kwararru a fannin tsaro a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.
Cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Gwamna, mai suna Yusuf Idris ya fitar jiya Lahadi, ya ce gwamna ya tafi Saudiyya ya yi Umra, kuma daga nan zai yada zango a Dubai inda zai hadu da wasu kwararru a fannin magance tsaro domin su tattauna hanyoyin shawo kan matsalar.
“Gwamna zai gana da masana fannonin tsaro a Dubai domin neman shawarwarin hanyoyin da suka fi dacewa a kawo karshen wannan hare-hare, kashe kashe sa samamen garkuwa da mutane da suka addabi jihar Zamfara.
“Sannan kuma ana sa ran zai gana da jami’an gwamnatin Saudiyya domin tattauna yadda za a sako wani malami dan asalin Jihar Zamfara, mai suna Alaramma Ibrahim.
“Ana tsare ne da Ibrahim kimanin shekaru biyu bayan da aka yi zargin ya shiga kasar Saudiyya da kwayoyi.
“Daga binciken da mu ka yi, an kama shi ne sanadiyyar wani tuggu da aka shirya masa, inda aka saka kwaya a cikin kayan sa, a Filin Jirgin Malam Aminu Kano.
“A Dubai kuma gwamna zai gana da jami’an Bankin Raya Kasashen Afrika (ADB) da wasu masu zuba jarin da ke da muradin zuba jari wajen inganta tattalin arzikin Zamfara.” Inji sanarwar.
Daga hawan gwamnan a ranar 29 Ga Mayu, Matawalle ya yi kokarin ganin an kawar da matsalar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.
Discussion about this post