KANO: Yadda caccaka da tsatstsaga ta sa Gwamnatin Ganduje janye gayyatar matan Sarki

0

Shugaban Hukumar Sauraren Kararraki da Zargin Rashawa na Jihar Kano, Muhuyi Magaji, ya bayyaa cewa an gayyaci matar Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da matan Sarkin Kano marigayi Ado Bayero a bisa kuskure.

An gayyace su ne da farko a bisa zargin su na da hannu wajen kashe naira bilyan 3.4 da gwamnatin jihar Kano ke binciken Fadar Sarki Muhammadu Sanusi.

Magaji ya shaida wa Kanmdfanin Dillancin Labarai NAN cewa yayin da suka gano cewa cikin wadanda ake gayyata har da matar Sarki da matan Sarki Marigayi Ado Bayero, sai suka janye dukkan gayyatar da suke yi wa mutane 29 da a farko suka ce hukumar ta na gayyata domin su yi bayanin wadansu kudade da suka karba domin kula da lafiyar su.

PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda hukumar ta zargi Sarkin Kano da kashe kudin. Sannan kuma ta buga labarin yadda Sarki ya kare kan sa da masarautar sa cewa bai yi facaka da ko sisi ba.

Fadar sa ta maida amsa cewa naira bilyan 1.8 ta samu a asusun masarautar a lokacin da Sarki Muhammadu ya kama sarauta, ba naira bilyan 3.4 kamar yadda aka yi zargi ba.

Daga nan sai masarautar ta nemi kotu ta dakatar da binciken. Sau biyu kenan kotu na bada umarnin a tsaida binciken.

’Yan Najeriya sun hakkake cewa Ganduje na yi wa sarki bi-ta-da-kulli ne saboda tunanin da gwamnan ke yi Sarkin bai goyi bayan sa a zaben 2019 ba.

Ganduje, wanda ya sake lashe zabe ta hanyar zaben da bai kammalu ba, wanda aka sake a wasu mazabu, ya yi nasara ce a yanayin da jama’a da dama a kasar nan da ma kungiyoyin sa-ido na Turai da na gida ke ikirarin an tabka harambe da hauragiya.

A yanzu dai dan takarar da aka kayar, Abba Yusuf, wato Abba Gida-gida da jam’iyyar sa PDP sun maka Ganduje da APC kotun daukaka kararrakin zabe, sun a kalubalantar nasarar da Ganduje ya yi.

Gigiwar aika wa matana sarki takardar gayyata

Matar Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi da matan marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero su biyu, na cikin mutane 29 da hukumar Muhuyi Magaji ke shugabanci ta aika wa sammacin gayyata domin su yi bayani.

Baya ga su kuma, akwai wasu ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano Bayero, mahaifin Ado Bayero, wadanda ke rike da sarautun gargajiya kuma sun manyanta.

Ganin sunayen wadannan rukunin matan saraki da kuma dattawa jinin Sarki Bayero, mahaifin Ado Bayero, ya harzuka milyoyin jama’a musamman a Kano, inda suka fara cewa to abin na Gwamna Ganduje ya wuce gona da iri kuma.

Masu kallon da farko Ganduje na fada da Sarki Muhammadu Sanusi ne, sun dawo su na cewa to an dawo kuma ana so a tozarta Gidan Dabo baki daya, har da zuri’ar Sarki Ado Bayero kan ta, wadanda a cikin su babu dan sa da ya samu sarauta Sarkin Kano bayan rasuwar sa.

Dama kuma da dama a baya na kukan cewa Ganduje ya na kokarin raba kan Gidan Sarautar Kano ne, domin ya cimma manufar yaki da Sarkin Kano.

Babban dalilin haka kuwa shi ne, yadda daya daga cikin ‘ya’yan Ado Bayero, Aminu Ado Bayero ya karbi sarautar Sarkin Bichi, duk kuwa da cewa Ganduje ya yi wa kanin sa, Nasiru Ado Bayero tayin daya daga cikin masarautu biyar da aka kirkoro, amma ya ce ba ya so.

Fitowar wannan takardar bincike ta fusata hatta wasu da suka goyi bayan kirkiro da masarautun da Ganduje ya yi.

Hakimin Kura, ya yi kira ga sabon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero da ya ajiye wa Ganduje sarautar da ya lakaba masa, ya dawo ya goya wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi baya, domin su kare martaba da darajar Gidan Dabo, wadda ’yan siyasa ke kokarin zubar wa kima da martaba.

A gidajen radiyo da jaridu da kafafen sadarwa na soshiyal midiya, an rika tsatstsaga da caccakar Ganduje jim kadan bayan fitar takardar sammacin a hannun jama’a.

Wani basarake mai fada-a-ji a kafafen yada labarai da soshiyal midiya da kuma masarautar Kano, ya bayyana cewa:

“Ina cike da mamakin yadda Muhuyi Magaji ke ji-ji-da-kai da tinkahon wuce-gona-da-iri, wajen kokarin sa na kaskantar da masu daraja.” PREMIUM TIMES ta boye suna sa.

Magaji ya ce an yi saurin janye gayyatar ce, amma za a nemi ba’asin adadin da ake ganin cewa sun salwanta domin tantancewar da ake yi a binciken da hukumar ke yi.

Sai dai kuma duk irin tsantsenin binciken da za a yi, abin ba zai yi tasiri a idon jama’a ba, ganin yadda shi kan sa Gwamna Ganduje ke fama da shan caccaka, habaice-habaice, zolaya da shagube dangane da da yadda bidiyo ya nuno shi ya na jida da lodar milyoyin daloli ya na cusawa aljifan sa.

Ko cikin wannan makon sai da wata kotu ta daure wani fitaccen mawaki tsawon shekaru biyu, saboda ya ragargaji Ganduje a cikin wata waka da ya yi.

Da yawa na ganin cewa borin-kunya ne gwamnatin Ganduje ke yi a kan Sarkin Kano, domin Hausawa na cewa “mai bunu a gindi ai ba ya kai gudummawar kashe gobara.

“Bayanan da mu ke bincike na wasu alkaluma ne da aka ce an kashe adadin kudaden wajen neman magani, kuma ga sunayen wadanda aka ce an kashe wa kudaden a rubuce. Shi ne muka gayyace su, amma ba mu san akwai sunan matar sarki a ciki ba.”

Duk da an rigaya an janye takardar gayyatar, abin ya rage wa Ganduje goyon baya daga kokarin da gwamnatin sa ke yi wajen binciken kudaden da gwamnatin ta ce an kashe a masarautar Kano.

Da dama kuma a yanzu sun koma su na zargin Ganduje da kokarin tozarta Gidan Dabo, wanda a tunanin wasu da farko, da Sarki Muhammdu Sanusi kadai ya ke yaki.

Share.

game da Author