Duk wanda ya batar da takardar shaidar WAEC ba za mu sake masa wata ba – Hukumar WAEC

0

Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare (WAEC), ta ja kunnen jama’a cewa kowa ya adana takardar sa ta shaidar kammala karatun sakandare, domin daga yanzu ta daina sake wa kowa shaidar kammala sakandare.

WAEC a ta bakin Shugaban Ofishin Hukumar da ke Lagos, Olu Adenipekun, ta ce babu ruwan ta da sauya wa kowa takardar WAEC idan ta bata, ko ruwa ta ci ko ya lalata ta ko kuma idan gobara ta kone na.

Adenipekun ya ce wannan shawara ta zama dole saboda irin yadda jama’a barkatai ke kwarara ofishin hukumar su na kai korafe-korafen bacewa satifiket din su na kammala sakandare.

“ Bari na kara yi wa jama’a bayani dalla-dalla. Sau daya mu ke bada satifiket, ko ma na waye ya bace mun daina sake wa kowa na sa. Wannan ita ce gaskiyar magana.

“ Ba mu bayar da satifiket na kammala sakandare, wato WASSCE har sau biyu. Sau daya muke bayarwa, kuma dayan za mu rika bayarwa.

“ Amma idan mu ka yi bincike muka tabbatar da cewa lallai akwai inda mutum ba sakaci ne ya yi ba, kamar ambaliya ko wata gobara, to za mu iya sabunta masa wani.

“ Saboda kamar shekaru biyar da suka gabata mahukuntan wannan hukuma sun yi taro suka ce an daina bayarwa sau biyu, domin babu wata hukuma da ke bada satifiket har sau biyu.

Ya ce WAEC ta kammala shirye-shiryen bayar da takardar amincewa da mutum ya zauna jarabawar kammala sakandare idan ta sa ta bace, amma ba satifiket ne za su sake bayarwa ba.

“Kuma wannan shaidar ce muke ta bayarwa tun shekara biyar da ta wuce.

Hukumar ta ci gaba da cewa a yanzu satifiket din da suke bayarwa ya na da inganci da kuma wata ledar da ko ruwa ya fada ba zai dagargaje ba.

Share.

game da Author