Rahoton Tarayyar Turai kan zaben 2019 ya burge mu – PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana jinjina ga Wakilan Sa-ido kan zaben 2019 na Tarayyar Turai, dangane da bayanan ta a kan yadda zaben 2019 ya gudana a fadin kasar nan.

Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar PDP ne da kan sa ya yi wannan jinjina a cikin wani bayani da kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar jiya Lahadi a Abuja.

Olagbondiyan ya jinjina wa Tarayyar Turai dahngane da yadda ta fito ta fadi gaskiyarc abin da ya faru a lokutan zaben a fadin kasar nan.

Ya ce abubuwan da rahoton Tarayyar Turai ta fallasa ya kara tabbatar da zarge-zargen da jam’iyyar PDP da milyoyin ’yan Najeriya suka yi a kan yadda zaben ya gudana.

Ya ce irin yadda Tarayyar Turai ta rika bayyana dalla-dallar yadda aka yi karma-karma a lokutan zaben, ya kara gaskata tambayoyi da tababar da ‘yan Najeriya ke nunawa dangane da zaben.

Daga nan sai ya kara da cewa yanzu duniya za ta tabbatar da cewa ba wai a banza jam’iyyar PDP ta rika kukan cewa an yi mata magudi ta hanyar rage mata kuri’u ba.

“Har yanzu ‘yan Najeriya na cike mamaki da firgicin ji da karanta bayanan da Tarayyar Turai ta rika fallasawa a kan yadda “aka soke kuri’u kamar milyan 2.8 ba tare da gamsasshen dalili ba. da kuma yadda jami’an Hukumar Zabe ba su bada wani dalilin sokewar ba.

Ya kuma yi bayanin yadda aka samu “bambancin masu rajista har adadin milyan 1.66, kamar yadda hukumar zabe ta bayyana a ranar 14 Ga Janairu, idan aka kwatanta da wadanda jami’an zabe suka bayyana a wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa.”

Ologbbondiyan ya kuma ce rahoton EU ya fallasa yadda aka yi harkallar akwatinan zabe, yadda kayan zabe suka yi layar-zana, yadda “aka rika kin yi wa rajistar mai jefa kuri’a alamar ya jefa kuri’a” da kuma aka rika kin bin tsarin tantance mai jefa kuri’a a tsarinn gar-da-gar kamar yadda ya ke a ka’idance.”

Daga nan ya ce rahoton EU ya kuma tona asirin yadda jami’an tsaro suka rika yin yadda suka ga dama da kuma yadda aka rika yin amfani da su ana yi wa magoya bayan PDP barazana. s

Share.

game da Author