Darektan Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Barno, Usman Kachalla ya bayyanawa manema labarai ranar Litinin cewa mutane 30 ne suka rasu a harin kunar bakin wake da aka kai garin Mandarari dake Karamar Hukumar Konduga, Jihar Barno.
Kachalla yace wasu ‘yan kunar bakin wake su uku ne suka afka wani teburin mai shayi da yake hade da gidan kallon fina-finai suka tada bama-baman dake daure a jikin su.
” A bayanan da muka samu, nan take mutane 17 suka riga mu gidan gaskiya, sauran 13 kuma suna rasu bayan haka ne a dalilin samun kula cikin gaggawa.
” Bamu samu daman isa har can inda abin ya faru ba saboda sojoji sun datse hanyoyin shiga garin domin tsaro.
Su dai wadannan ‘yan kunar bakin wasu, ance su uku mata biyu da namiji daya.