Binta Kofar Soro ta rasu

0

Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Binta Kofar Soro ta riga mu gidan gaskiya.

Hajiya Binta, kamar yadda abokanan aikinta ke kiranta da shi, ta rasu ne ranar Asabar da safe sannan anyi jana’izan ta a garin Kano.

Jarumi kuma fitaccen dan wasa, Nuhu Abdullahi ne ya tabbayar wa PREMIUM TIMES da rasuwar Binta.

” Lallai Hajiya Binta ta rigamu gidan gaskiya a yau Asabar. Farfajiyar fina-finai na Kannywood ta yi rashi matuka domin ba a wasa ba ma kawai Hajiya Binta uwace garemu ba ki daya.

Ali Nuhu, Rahama Sadau da sauran abokanan aikin ta duk sun bi marigayiyar da addu’o’in Allah ya sa ta huta.

Wasu da dama ma sun canja hotunan su zuwa hoton marigayiyar.

Allah ya ji kanta, Amin.

Share.

game da Author