#PHC4UHC: Buhari ya dora wa NIPSS nauyin tsara hanyoyin samar da ingantaccen kiwon lafiya a Najeriya

0

Kamar yadda aka saba duk shekara kungiyar NIPSS kan dauki nauyin yin nazari domin baiwa gwamnati shawarwarin hanyoyin da suka fi dacewa domin shawo kan matsalolin kasan.

A wannan shekara Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora wa wannan kungiyar nauyin tsara hanyoyin da za su fi dacewa gwamnati ta bi domin samar da kiwon lafiya mai nagarta a kasar nan.

Tun farko NIPSS ta gano cewa matsalar rashin kudi ne babban matsalar dake ci wa fannin kiwon lafiyar kasar nan tuwo a kwarya.

A dalilin haka kungiyar ta amince ta ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko dake jihohi shida a kasar nan domin gano matsalolin da suke fama da shi.

Jagoran kungiyar Nasirudeen Usman ya bayyana haka a ziyarar da kungiyar ta kai ofishinin sa a Legas.

Sakataren gwamnatin jihar Tunji Bello ya bayyana cewa samar da kiwon lafiya mai nagarta wa mutane da tsara hanyoyin samar da kudaden da za a bukata wajen yin haka hakin gwamnati ne.

Bello yace a dalilin haka gwamatin jihar ke kokarin ganin ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.

Sanin kowa ne cewa tsarin samun kiwon lafiya mai nagarta a Najeriya daidai yake da Karin maganan da ake cewa ‘iya kudin ka iya shagalinka’. Ma’ana kiwon lafiya a kasar nan ya danganta da nauyin aljihun mutum.

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) tayi ya nuna cewa Talauci da yayi wa mutanen najiyar Afrika katutu ya jefa mutane da dama cikin matsanancin fama da matsalar kiwon lafiya.

Shugaban asibitin koyarwa na jami’ar jihar Legas Adetokumbo Fabamwo ya bayyana cewa kashi 70 bisa 100 na mutanen Najeriya sun tsinci kansu a cikin wannan hali ne saboda fannin kiwon lafiyar kasar nan ba za ta iya samar musu da kiwon lafiya nagari ba.

A karshe ministan kiwon lafiya Isaac Adewole yace gwamnati ta dauki matakan da za su taimaka mata wajen ganin ta kawar da matsalolin rashin kudi a fannin kiwon lafiya da yawan kudaden da mutanen kasar ke kashewa domin samun kiwon lafiya mai nagarta.

Share.

game da Author