Mutane miliyan 150 za su iya kamuwa da cutar mantuwa ‘Dementia’ nan da shekara 30 a duniya – WHO

0

Cutar mantuwa ‘Dementia’ cuta ce dake kama kwakwalar mutum inda mutum zai fara mantuwa ko kuma rudewa kafin ya tsufa.

Likitoci sun bayyana cewa samun rauni a kai, rashin cin abincin dake inganta garkuwar jiki, yawan shan magani haka kawai, zukar taba sigari, shan giya na cikin hanyoyin dake hadasa cutar.

Sakamakon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa a yanzu haka mutane miliyan 50 ne a duniya ke dauke da wannan cuta.

Alamun cutar sun hada da yawan mantuwa, rashin iya yin zurfin tunani ko kuma yanke hukunci, rashin iya magana yadda ya kamata, rashin iya gane mutane da sauran su.

WHO ta kuma ce nan da shekaru 30 masu zuwa adadin yawan masu fama da wannan cutar zai iya karuwa zuwa miliyan 150 a duniya idan ba gaggauta daukan mataki akan cutar ba.

A Nahiyar Afrika sakamakon binciken ya nuna cewa mutane miliyan 2.13 na dauke da cutar sannan nan da 2050 adadin yawan mutanen dake dauke da cutar zai iya kaiwa miliyan 7.62.

A dalilin haka shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya yi kira ga gwamnatocin duniya kan tsara kudirori da zasu taimaka sannan da daukan mataki don hana yaduwar cutar.

Ghebreyesus ya ce ma’aikatan kiwon lafiya za su iya wayar da kan mutane kan hanyoyi gujewa kamuwa da cutar.

Hanyoyin gujewa kamuwa da cutan sun hada da:

1. Motsa jiki.

2. Rage yawan shan zaki.

3. Kiyaye hanyoyin kamuwa da cutar siga da hawan jini.

4. Gujewa shan giya da miyagun kwayoyi.

5. Gujewa zukar taba sigar.

6. Cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki.

7. Gaggauta samun kula da zaran an sami rauni a kai.

8. Rage yawan shan magungunan musamman wadanda ake sha ba tare da umurnin likita ba.

Share.

game da Author