Hukumar Tsaro ta Sojoji Saman Najeriya ta bayyana cewa zaratan ‘Operation Diran Mikiya’ tare da hadiguiwar sojojin Bataliya ta 271, sun kashe ’yan bindiga 12 da Dajin Kamuku, a yankin Birnin Gwari, Jihar Kaduna.
Sojojin na sama sun kara da cewa sun kuma samu nasarar kubutar da mutane 15 da aka yi garkuwa da su a hannun ‘yan bindigar.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar Sojojin Sama, Ibekunle Daramola, shi ne ya bayyana haka jiya Talata a Abuja.
Daramola ya kara da cewa kafa Bataliyar Sojojin Sama ta 271 da aka yi a Dajin Birnin Gwari ya na samun gagarimar nasara sosai.
A cewar sa, an kashe maharan su 12 ne ta hanyar farmakin da aka kai musu daga sama.
Ya ce an kai farmakin sintiri ne a Dajin Kamuku na cikin yankin Birnin Gwari da kuma cikin yankin Karamar Hukumar Sabuwa, ta jihar Katsina.
“Farmakin da aka kai wa mahara ya sa sun gudu suka warwatsu, hakan ya sa wadanda suka yi garkuwa da su samun damar kubuta, wasu suka gudu zuwa Nacibi, wasu Gobirawa wasu kuma Dungun Muazu cikin Karamar Hukumar Birnin Gwari.”
Daramola ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sojojin sama za su ci gaba da aiki tare da sojojin kasa domin ganin an kakkabe mahara a Arewa maso Yamma.