Bincike ya nuna cewa matasa da dama ne a fadin duniya ke kashe kawunan su a dalilin ta’ammali da muggan kwayoyi.
Likitocin dake asibitin yara na kasa dake Columbus, Ohio da wadanda ke cibiyar gudanar da bincike kan illar shan guba dake kasar Amurka ne suka gano haka.
Sakamakon ya nuna cewa matasa masu shekaru 10 zuwa 24 akalla miliyan 1.6 sun mutu a dalilin shaye-shayen guba.
Sannan matasan da suka mutu a dalilin shan muggan kwayoyi sun ninka wannan yawan sannan a ciki kuma mata ne suka fi yawa.
A dalilin haka masu binciken ke kira ga gwamnatocin duniya da su maida hankali wajen kula da yara manyan gobe.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya sakamakon binciken cibiyar yaki da sha da Ta’ammali da muggan kwayoyi na majalisar dinkin duniya (UNODC), NBS, cibiyar (CRISA) da EU ya nuna cewa akalla mutane miliyan 14.3 na ta’ammali da kwayoyi a Najeriya.
EU ta gabatar da sakamakon wannan bincike ne ranar Talata a Abuja inda ta kara da cewa adadin yawan mutanen dake Ta’ammali da Kwayoyi a kasar nan ya fi adadin yawan mutanen dake wasu kasashen turai.
Sakamakon ya kuma nuna cewa ‘yan shekaru 15 zuwa 64 ne suka fi shiga cikin wannan matsalar sannan a cikin mutane hudu dake fama da wannan matsalar daya mace ce.
Bayan haka binciken ya kuma kara nuna cewa kwayoyin da amfani da su ya zama ruwan dare a kasar nan sun hada da hodar ibilis, tabar wiwi, kayar tramadol da maganin tari kodin sannan kuma a Arewacin Najeriya ne abin yafi muni.
Wani malami a jami’ar Bayero dake Kano, mai Mainasara Yakubu Kurfi a nazari da yayi kan matsalolin shaye shayen miyagun kwayoyi yace za a iyakawo karshen wannan matsala ne idan iyaye da malaman makarantar muhammadiyya da ta boko da sauran al’umma suka tashi tsaye wajen tarbiyantar da yara da matasa tun daga gidaje da makarantu da kuma cikin unguwanni.
Ya kuma ce ya zama wajibi matashi yayi nazari sosai wajen lura da irin abokan da yake mu’amulla dasu. Bin Magana da shawarwarin iyaye wajibi ne ga matashi ma dammar yana son ci gaban rayuwarsa da zaman lafiya. Haka kuma, maida hankali wajen neman ilimin addini da na boko wajibi ne. Maimakon yawace-yawace a layuka da lungunan unguwanni, neman sana’a maimakon zaman kasha wando abu ne mai kyau ga matashi.