Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa jami’an sa na nan na ta kokarin ganin sun dakile matsalar tsaro a fadin kasar nan.
Ya kuma kara da cewa ana bakin kokarin hukunta dukkan ‘yan sandan da ake kamawa da laifi.
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ne ya bayyana haka bayan ganawar da Majalisa ta yi da Sufeto Janar Adamu a yau Talata.
Adamu ya amsa gayyatar majalisa ne dangane da yawaitar garkuwa da mutane da ake ta yi babu kakkautawa a fadin kasar nan, musamman a Arewa.
Ya bayyana a Majalisa ne tare da Mashawarcin Shugaban Kasa a Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enang, da kuma wasu manyan jami’an ‘yan sanda.
Tun na ranar 25 Ga Afrilu ne aka gayyaci Adamu, domin neman shawarwarin yadda za a kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane da ake ta yi a kasar nan.
Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ne ya bada shawarar gayyatar sa, ganin yadda ake yawan ngarkuwa da mutane, har aka kashe wata ‘yar kasar Birtaniya a garin garkuwa da mutane a Jihar Kaduna.
A yau Talata kuma Adamu ya halarci gayyatar, inda aka rufe kofa da shi, aka yi ganawa ta tsawon sa’o’i biyu.
Bayan ganawar ce Saraki ya ce Adamu ya yi musu bayanin kokarin da jami’an tsaro ke yi dangane da hare-hare, garkuwa da mutane, fashi da makami, ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.
Saraki ya ce Sufeto Janar Adamu ya yi alkawarin za a kara matakan tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.