Sarkin Katsina Abdulmumini Usman ya aika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakon tare da yin kira ga reshi da ya maido hankalinsa matsalar rashin tsaro da ya addabi mutanen jihar da kasa baki daya.
Sarki Kabir ya bayyana haka ne a wajen taron samarwa manoman jihar irin auduga da kayan aikin gona wanda ministan Gona Audu Ogbe da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emiefile suka halarta.
” Ba iri bane ya dame mu yanzu a jihar Katsina, tsaro shine yafi tada mana hankali. Manoma da dama sun arce daga gonakinsu haka suma makiyaya duk sun rasa matsuguni a dalilin ayyukan mahara da masu garkuwa da mutane. Wanna shine ya fi damun mu.
” Kusan kullum sai an kawo mun rahoton ko an kashe wani ko kuma an yi garkuwa da mutane a kauyukan mu. Ina dadi a haka. Ku je ku gaya wa shugaban kasa cewa duk kyawon wadannan shirye-shirye ba za suyi tasiri ba idan babu tsaro. Mu yanzu a gaskiya tsaro shi ya fi damun mu.
” Tsakani da Allah ace wai mahara su shigo har cikin garin Daura su yi garkuwa da babban basarake kamar Magajin Gari. Aiko kasan akwai tashin hankali matuka. Yanzu fa babu wanda yake cikin tsaro, yau ko kana gidan ka ne koko bisa hanya, hankalinka a tashe yake. Haba dai wannan ko wacce irin kasa ce?”
Idan ba a manta ba dan majalisar tarayya dake wakiltar safana ya yi irin wannan kuka a zauren majalisa a makon da ya gabata.
Hon. Safana ya yi wannan korafi ne a Zauren Majalisar Tarayya, inda ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta kai dauki a kananan hukumomin Safana/Batsari/Danmusa, inda mahara ke ci gaba da kashe mutane, garkuwa da kuma lalata dukiyoyin jama’a.
“Ba kawai su ke yi su na banka wa gidaje wuta, su saci mata da mazaje wadanda ba su da karfi, su kuma majiya karfin su bi su su karkashe. Yanzu kauyuka hudu a mazaba ta na fama da wannan tashin hankali na hare-hare.
“Sun kai wa kauyukan Massa, Alhazawa da Guzurawa hari inda suka karkashe mutane da kona gidaje da dukiyoyin su.
“Jiya-jiyan nan kuma sun je har cikin kauyen Gobirawa a Karamar Hukumar Safana, suka kashe mutane 12, suka kona gidaje da dukiyoyi.
‘Yan Majalisa da dama sun yi tir da yadda ake ta yawan kashe-kashen jama’a musamman a karkara, amma hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya ta kasa yin wani hobbasa.