Daga yanzu za a rika rubuta shekarun haihuwa a satifiket din NYSC

0

Hukumar kula da jindadin masu yi wa kasa hidima NYSC ta bayyana cewa daga yanzu za ta fara rubuta shekarun haihuwa a satifiket din kammala hidiman.

Shugaban hukumar Shuaibu Ibrahim ya sanar da haka a taron wayar da kan masu yi wa kasa hidima daga aka yi a Abuja ranar Talata.

Ibrahim yace hukumar ta dauki wannan shawara ne domin hana masu karyar shekarun su na haihuwa domin samun damar yi wa kasa hidima din.

” Hukumar shirya jarabawar kammala makarantar sakandare ta yammacin Afrika (WAEC) ta bayyana cewa da dama daga cikin daliban da NYSC ke horas wa na yin karya ga shekarun su na haihuwa domin samun damar shiga shirin.

Haka kuma Ibrahim yace hukumar zata rika rubuta shekarun haihuwa a satifiket din da ake bai wa wadanda shekarun su ya wuce shekarun yi wa kasa hidima din.

Ibrahim ya yi kira ga duk hukumomin shirya tarabawa da su dauki wannan mataki da muhimmanci maruka domin hanawa da bankado masu karyarshekarun su na haihuwa a kasar nan.

Share.

game da Author