Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ya yi wurgi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wanda ta soke cancantar takarar Ademola Adekele, dan takarar gwamna da ya yi takarar zaben Osun a karkashin jam’iyyar PDP.
Da ta ke yanke hukunci a yau Alhamis, kotun ta ce Kotun Tarayya ta tafka kuskure da ta soke takarar Adeleke, “alhali hujjoji a gaban kotun sun nuna cewa ya cika sharuddan da dokar kasa ta gindaya masa na tsayawa takara.”
Kotun Daukaka Kara ta ce shaidar da shugaban makarantar da Adeleke ya gabatar dangane da satifiket na kammala karatun sa, ta wadatar a ce ya cika sharuddan da doka ta gindaya na shiga takarar gwamna.
Kotun ta ce Babbar Kotun Tarayya ta tafka kuskuren korar Adeleke daga cancantar shiga takara, ba tare da yin la’akari da shaidar da shugaban makarantar da ya kammala ba.
Har ila yau, Kotun Daukaka Kara ta ce tun farko ma Babbar Kotun Tarayya ba ta ma da hurumin da za ta saurari karar, tunda batun da ake magana abu ne da ya shafi jihar Osun.
A yanzu dai a wata shari’ar kuma, Adeleke na kalubalantar nasara da APC ta yi a zaben gwamnan jihar.
Shari’ar na a gaban alkalan Kotun Koli.