Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa daga yanzu baza ta sake yin amfani da kamfanonin dake biyan asibitocin dake karkashin shirin inshorar Lafiya ba, wato HMOs a sabon tsarin inshoran kiwon lafiya ta jihar.
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Makusidi M.M. ya sanar da haka a Minna a ziyara da kungiyoyin NIPSS da DRPPC suka kawo wa jihar.
Makusidi yace gwamnati ta yanke hukuncin haka ne adalilin rashin biyan asibitocin dake karkashin shirin inshoran kiwon lafiya da wadannan kamfanoni ke yi.
” Tun da aka kafa shirin inshoran kiwon lafiya ta kasa wadannan kamfanoni sun karbi akalla Naira biliyan 350 amma duk da haka mutane kalilan ne ke cikin tsarin kuma ma basu samun kula yadda ya kamata.
Ya ce a dalilin haka mutane musamman talakawa basu amfana da shirin yadda ya kamata.
” A yanzu haka gwamnatin jihar ta kafa nata sabon shirin inshoran kiwon lafiya domin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen jihar mai suna ‘Niger state Contributory Health Scheme (NGSCHS)’
A karshe ya ce babban burin gwamnatin jihar shine ta ga mutane musamman talakawa na samun kiwon lafiya kamar kowa.
Discussion about this post