A Laraba ne wata majiya ta sanar wa PREMIUM TIMES cewa mahara sun bindige dagacin Balle Aliyu Ibrahim.
Balle kauye ce dake karamar hukumar Gudu a jihar Sokoto.
Majiyar ya bayyana cewa wannan abin tashin hankali ya farun ranar Talata bayan maharan sun diran wa kauyen a bisa Babura suna harbi ta ko ina babu tsagaitawa.
Ya ce a dalilin haka mutane kowa suka yi ta kansu.
” Daga zuwan maharan sai suka nausa fadan dagacin inda suka tadda kofar shiga fada a garke da kwado. A dalilin haka wasu suka tallaka ta katangan fadan sannan wasu na jira a kofar fadan.
” Daga shigan su kuwa sai suka harbe basaraken mai suna Aliyu har lahira sannan suka garzaya ofishin ‘yan sandan dake yankin suka bankawa motoci da ofishin wuta.
Wasu mazaunan garin sunce maharan sun tsallako ne daga kasar Nijar suna masu cewa akwai yiwuwar sun far wa basaraken ne domin daukar fansa bisa wani abu da ya hada su.
” Dama dagacin ne ya kai kara wajen hukuma game da miyagun aiyukkan da wadannan maharan ke yi a yankin mu.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar batace komai akan wannan hari.
Sai dai kuma bayanai sun nuna cewa rundunar sojin Najeriya ta hana yin amfani da Babura a jihohin arewacin Nijeriya bakwai.
Discussion about this post