TAMBAYA – Wani sallah ne cikin salloli 5 aka fi so mutum ya rika dagewa ya na yi akan lokaci? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA – Wani sallah ne cikin salloli 5 aka fi so mutum ya rika dagewa ya na yi akan lokaci ?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Duk salloli biyar na wajibi tillas ne musulmin kwarai ya kiyayesu kuma ya gabatar dasu cikin lokaci kuma a cikin Jam’i (ga maza). Sallah
itace ginshikin addini kuma mafi girman ibada. Tsaida sallah akan lokacinta shi ne mafi girman abinda Allah yafi so a cikin ibadu.

Mallamai suna ganin cewa salloli uku daga cikin biyar dinnan sun fi tsananin bukatar kiyayewa, sabo da nassoshin da suka tabbata wanda ke
kara karfa tsare lokacinsu. Wadannan salloli su ne:

1) Sallar Asubahi.
2) Sallar Isha’i .
3) Sallar La’asar.
4) Sallar Asubahin ranar Juma’a.

Ya kai dan uwa musulmi!!! Lalle Sallah itace fakon abinda za’a yi maka hisabi akai, idan ta cika, to sauran masu sauki ne. Amma idan
batacika ba, to dan Adam ya tabe kuma yayi asara. Akarshe kasani duk sallar da ba’a yita akan lokacin taba, to Allah baya karbanta.

Allah shi ne mafai sani.

Share.

game da Author