An yi garkuwa da su ’yan kasar Chana su biyu a cikin Jihar Ebonyi da ke Kudu maso gabacin Najeriya.
An yi garkuwa da Sun Zhixin da Wang Quing Hu wadanda ke aiki da wan kamfanin gina titi na Tingyi.
An yi awon gaba da su a lokacin da suke duba aikin titi a cikin Karamar Hukumar Ohaozara, daga can wasu masu dauke da bindigogi suka yi awon gaba da su.
An ce wadanda suka sace su din, su na sanye da huluna masu sufe fuskoki. Kuma sun gudu da su ne wajen karfe 3:30 na ranar jiya Laraba.
PREMIUM TIMES ta ji cewa an sace mutanen biyu ne akauyen da ake kira Iva, bakin kogi, aka tilasta wadanda ke aikin fitowa daga cikin wani rami, daga nan suka gudu da su.
Oda Loveth, wadda ita ce Kakakin Hulda da Jama’a na jami’an tsaron jihar, ta tabbatar da sace mutnanen biyu.
Ta ce tuni an tura wasu zaratan jami’ai domin gano inda duk ta kasance ake tsare da su.