Barkewar sabon rikici ta sa gwamnatin Jihar Kaduna gaggauta kakaba dokar hana fita tun daga safe har wata safiya a Karamar Hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna.
Hakan ya biyo bayan rahotannin samun fantsamar tashe-tashen hankula a cikin kauyuka nan da can.
Har yanzu dai babu cikakken rahoton abin da ya faru ko ya ke faruwa a yankunan, amma dai gwamnati ta shana zirga-zirga tsawon awa 24 a yankin.
Kakakin Yada Labarai na Gwamna Nasir El-Rufai, mai suna Samuel Aruwan ne ya fitar da sanarwar kakaba dokar, a wani shafin sa na Facebook.
“Sakamakon abin da ya faru a Kasuwar Magani, Gwamnatin Jihar Kaduna na sanar da kakaba dokar hana fita awa 24 a Karamar Hukumar Kajuru, har sai abin da hali ya yi.”
Kasuwan Magani da wasu yankunan Karamar Hukumar Kajuru da Kudancin Kaduna ya sha fama da rikice-rikecen da suka hada da kai hare-hare da kuma maida farmakin daukar fansa.
Daruruwan jama’a sun rasa rayukan su sakamakon rikice-rikicen da ya shafi fadan kabilanci da na addini.
Discussion about this post