An cafke dan sandan da ya tozarta wani fasinja don ya mallaki wayar iPhone mai tsada

0

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta, ta bada sanarwar damke wani dan sanda bayan an nuno shi a wani bidiyo ya ci zarafin wani fasinja saboda ya mallaki iPhone ta Naira 200,000.

Al’amarin ya faru ne ranar Talata, a Okpe, Jihar Delta, kamar yadda wanda ya watsa bidiyon a twitter ya bayyana.

An nuna bidiyon mai tsawon dakika 44, inda aka nuno dan sandan mai mukamin sajen, ya tare wata motar fasinja, yayin bincike.

An nuno wayar matashin fasinjan a hannun dan sandan, inda ya ke tambayar sa nawa ya saye ta?

An kuma ji muryar mai wayar ya ce masa Naira 200,000 ya sayi wayar. Daga nan ne sai dan sandan ya rika jujjuya wayar ya na cewa:

“Kun gani ko? Ga shi da wayar naira 250,000 amma ni da na shekara 13 ina aiki ba zan iya sayen irin wannan waya mai tsada ba.”

Daga nan sai aka ji ya na cewa fasinjan ya fito daga cikin mota. Sannan kuma ya fasa wayar a kasa.

Rahotanni dai sun ce sauran fasinjoji ba su bari ya tafi da mai wayar ba.

To da yammacin jiya Laraba kuma sai Hukumar ‘Yan Sanda ta bada sanarwar kama wanda ya tozarta fasinjan, tare da cewa ya na nan tsare a gadurun, a Jihar Delta.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar ya ce za a hukunta shi, kamar yadda doka ta tanadar.

Jama’a da dama na ta ci gaba da yin tir da abin da dan sandan ya aikata. Jin an kama wanda ya yi laifin, sai jama’a ke kara matsa lamba cewa lallai a bayyana fuskar sa domin a tabbatar da shi din ne aka kama, kuma gaggauta hukunta shi.

Share.

game da Author