TIRKA-TIRKA: Hukumar FRSC za ta fara tilasta wa masu karya dokar tuki yin aikin karfi da kwace lasisi

0

Hukumar Kiyaye Hadurra Kan Titi, wato FRSC, ta bayyana cewa daga ranar 1 Ga Yuni, za ta karfafa tare da tilasta kiyaye dokokin tuki ka’in-da-na’in.

Kakakin FRSC, Bisi Kazeem, ya shaida cewa Shugaban Hukumar, Boboye Oyeyemi ne ya bayyana haka a wani taro da hukumar ta shirya, a hedikwatar ta, da ke Abuja, jiya Laraba.

Oyeyemi ya ce daga yanzu ta a fito da tsarin Yawan Laifuka Yawan Hukunci. Wannan ya na nufin za a rika daukar matakai tsaurara ga wanda ya karyata dokokin tuki da yawa, ko kuma wanda aka tattara yawan laifukan da ya rika yi har aka ga abin na sa ya zama izgilanci da kuma raina hukuma.

Shugaban na FRSC, ya ce daga cikin hukunce-hukuncen da za a rika yanke wa direbobi, akwai maida direba komawa makarantar koyon tuki.

Sannan kuma ya yi karin bayanin cewa wani kuma idan na sa laifin karya dokar ya yi yawa, to za a tilasta masa yin aikin karfi a cikin al’umma.

Aikin karfi dai shi ne irin yadda a cikin wasu kasashe a ke sa mutum shara a kan titi da sauran su.

Sannan kuma FRSC ta kara da cewa:

Wanda ya aikata laifi daya zuwa 10, zai biya tara.

Wanda ya karya doka sau 10 zuwa sau 14, za a yi masa gargadi tare da cin sa tara.

Wanda ya karya doka sau 15 zuwa sau 20, za a kwace lasisin sa, a hana shi tuki har wani tsawon lokaci.

Wanda ya karya dokar tuki sau 21 abin da ya yi sama, za a kwace masa lasisi. A hana shi tuki kenan gaba daya.

Ya nuna damuwa dangane da yadda ake yawan karya dokokin tuki a Najeriya.

Share.

game da Author