Tsohon mai horas da kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane ya koma kungiyar, watanni 9 bayan ya yi bankwana da ita.
Ya yi sallama da Madrid watanni kadan bayan bayan ya yi nasararv daukar Kofin Zkarun Turai karo na uku a jere.
Tun bayan tafiyar sa Madrid ba ta sake tabuka abin a zo a gani ba.
An dauki Zidane a yau Litinin, kuma an sallami Santiago Solari. Zidane zai rike kungiyar daga nan har zuwa ranar 30 Ga Yuni, 2022.
Bayan lokacin idan ya ga dama zai ci gaba da rike kulob din a karkashin wata sabuwar kwangilar.
Rahotanni daga daga kulob din da kuma kafafen yada labarai na duniya sun ce shugaban Madrid, Florentina Perez ya ware wa Zidane fam na Ingila har milyan 300 domin ya sayo duk wani dan wasan da ya kwanta masa ko ma daga wane kulob ne.
Tuni dai ‘yan wasan Madrid wadanda ke da niyyar barin kulub din suka kwance kayan da suka rigaya suka dora a kai, kowa na murna.
Birnin Madrid ya barke da murna jin cewa Zidane ya koma Real Madrid.
Shugabannin Real Madrid sun tabbatar wa Zidane cewa babu wanda zai rika sa masa baki a dukkan hukuncin ya yanke a kan sha’anin ‘yan wasa,