Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana hujjoji da dalilan rashin kammaluwar zabukan gwamna a wasu jihohi jihohin da suka kunshi: Adamawa, Sokoto, Filato, Bauchi da kuma baya-bayan nan, jihar Benuwai.
Akwai kuma Jihar Rivers inda aka dakatar da bayyana sakamakon zabe, har sai ranar da aka sake aza wa, a bisa dalili na barkewar tashe-tashen hankula, kwacen akwatu, lalata takardun zabe, sace jami’an zabe da sauran rigingimun da suka dagula zabukan.
Haka ma a jihar Kano ana kan tankiya da rudanin neman yadda za a fitar da wanda ya yi nasara tsakanin dantakar PDP da na APC, Gwaman Abdullahi Ganduje.
Rudani ya kunno kai a Kano bayan da a cikin darenLitinin Mataimakin gwamna, Nasiru Gawuna ya kwashi zuga shi da daya daga cikin kwamishinonin Ganduje da Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa suka je Cibiyar Tattara Sakamakon Zaben Karamar Hukumar Nassarawa suka kekketa takardun sakamakon zabe.
Dama kuma ita kadai ce ba a bayyana sakamakon zaben na ta ba. Tuni dai ‘yan sanda suka cafke su tun jiya da dare.
ABIN LURA A WANNAN TANKIYA
Babban abin lura sannan kuma abin da ke ba masu adawa mamaki shi ne dukkan wadannan jihohi bakwai, duk PDP ce ke kan gaba, a daidai lokacin da INEC ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba.
A Jihar Filato an bayyana cewa sai an sake zabe a Kananan Hukumomi 13.
A jihar Sokoto kuwa, Gwamna Aminu Tambuwal ya tuma tsalle gefe daya, ya ce bai yarda da hukuncin INEC cewa zabe bai kammalu ba, musamman tunda shi ne ke kan rinjiye. Har ma Tambuwal ya garzaya kotu.
A jihar Bauchi kuma an ce sai an sake zabe a Karamar Hukumar Tafawa Balewa, duk da cewa PDP ta yi ikirarin cewa ba a tirsasa jami’in INEC bayyana sakamakon da ita PDP din ta yi nasara da babban rinjaye ba. har bidiyon yadda aka yi sanarwar sao da PDP ta rika watsawa soshiyal midiya.
A Jihar Kano kuma kuri’un Karamar Hukuma daya ake jira sannan a bayyana sakamako. Idan kuma kuri’un da aka soke ko suka lalace sun zarce adadin na wadanda na faya ya yi wan a biyu, to a nan ma INEC za ta iya cewa zaben bai kammalub ba kenan.
DALILAN DA KE SA RASHIN KAMMALUWAR ZABE
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa zabukan jihohin Adamawa, Bauchi, Sokoto, Filato, Rivers har da Kano bas u kammalu ba tukunna. A kan haka ne PREMIUM TIMES HAUSA kutsa kai cikin taskar adana bayanan INEC domin yi wa wannan kiki-kaka filla filla.
Ko da ya ke a Kano ba a kai matakin da ake ce zaben bai kallamalu ba, amma an tsaida sanarwar har sai an tantance sakamakon karamar hukuma daya.
MA’ANA TA FARKO: INEC na cewa zabe bai kammalu ba idan ratar kuri’un da wanda ya yi nasara ko wanda ke kan gaba da kuma wanda ya yi ta biyu, ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba. Don haka dama a rubuce ya ke a dokar INEC cewa idan hakan ta faru, to za a sake zabe a wasu rumfunan da aka yi tankiyar kuri’un da aka soke.
ME DOKAR ZABE TA INEC TA CE?
Dokar Zabe ta Sashe na 153 ta jaddada cewa matukar ratar yawan kuri’un wanda ya zo na daya shi da wanda ya zo na biyu ba ta kai yawan kuri’un da aka soke ba, to zabe bai kammalu ba, har sai an sake yin zaben raba-gardama a yankunan da aka soke kuri’un.
INA MATAKAN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
Cikin wata doguwar makala da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya taba gabatarwa, bayan hawan sa shugabancin INEC, ya ce:
INDA HARGITSI YA HANA A YI ZABE
“A zabukan da suka gabata can baya, ’yan siyasa kan hargitsa zabe a inda suke ganin ba su da karfin samun kuri’u, ta haka sai su yi nasara a yankin da suka fi karfi. A kan haka ne a yanzu sai INEC ta ce idan aka hargitsa zabe a ko’ina, to INEC za ta sake bai wa jama’ar wannan yanki damar sake jefa kuri’a. Saboda kuri’a ce a kasar nan ke zabar mutum, don haka tilas ita ce za ta yi aiki kenan.
INDA ZABE BAI KAMMALU BA TUN A MAZABU
“Sannan kuma akwai inda ake samun zabe bai kammalu ba tun ma a mazabu. Gaba dayan dalilin bayyana hakan shi ne domin a bai wa jama’a damar jefa kuri’ar su. Domin kuri’a ce abin amfani ko dogaro a wajen zaben shugabannni. To idan an fahimci abin da duk na bayyana, sai kuma mu dawo, shin me ya sa ake samun zabukan da ba su kammalu ba?
DALILAN SAMUN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
“Na farko dai akwai sabon sauyin canji a zabukan 2015, musamman sakamakon shigo da na’urorin zamani wajen zabe. Amma dai duk da hakan, ba mu kai ga matakin da ake son a cimma ba. A karon farko a zaben 2015 an samu karancin ratar kuri’u tsakanin jam’iyyar da ta yi nasara da kuma wadda aka kayar. Kuri’a milyan 2.5 ce mafi karancin yawan ratar kuri’u a zabukan shugaban kasa tun daga 1999.
“Na biyu kuma a da an saba ganin jam’iyyar da ta yi nasara na tserewa fintinkau da rata mai yawa sakamakon karfinta da kuma karancin karfin tarkacen kananan jam’iyyun adawa. Amma a yanzu kuwa akwai manyan jam’iyyu biyu masu karfi.
*“Na uku kuma, akan samu takara ta yi zafi sosai. Kun ga an samu gaggan ‘yan takara biyu da suka fito daga manyan jam’iyyu biyu kenan. Kun ga kenan akan samu inda manyan jam’iyyu biyu sun fito da gaggan ‘yan takara biyu.
*Wani dalilin kuma shi ne, yadda a yanzu zabe na kara samun inganci, inda a yanzu kuri’a ce ke tabbatar da sakamakon zabe. Duk inda ka duba sakamakon kowane bangare, za ka ga cewa ratar ba ta da yawa soasi. Wannan kuwa na nuna maka yadda takarar ke kara zafi sosai kenan.
RABE-RABEN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
Rabe-raben Rashin Kammaluwar Zabe, sun kasu gida uku, wadanda a Turance ake kira (i) Run-off Election); (ii) Re-run Election; (iii) Inconclusive Election.
Dukkan wadannan rabe-raben zabukan da ba su kammalu ba, ma’anar su dai daya ce, wato ba za a iya bayyana sakamakon zabe ba, har sai an sake zabuka a wasu mazabu, yankuna ko kananan hukumomi inda daya daga cikin wadancan sabubba uku na Turanci suka faru.
Sai dai kuma duk da cewa ma’anar ta su daya ce, wato sake yin zaben-raba-gardama a wasu mazabu ko rumfuna, wannan ma’anar ta yi rassa har guda uku, kamar yadda za a fayyace wa masu karatu dalla-dalla.
*Run-off Election: Wannan zaben-raba-gardama ne, wanda ake sake yi idan dan takarar gwamna ko na shugaban kasa ya kasa yi wa wanda ya zo na biyu ratar da ta wajaba a ce ya yi masa a fadin jihar, ko kuma kasa.
*Re-run Election: Shi kuma wannan zabe ne wanda ake sakewa yayin bayan wanda aka gudanar da farko ya hadu da magudi ko kuma an samu inda aka ki bin sharuddan da INEC ta gindaya a bi wurin yin zabe.
*Inconclusive Election: Zaben-raba-gardama ne, ake sakewa inda adadin yawan kuri’un da aka yi rajista a rumfunan da aka soke kuri’u za su iya samar da ratar da ake bukata wanda ya yi na daya ya bai wa wanda ya yi na biyu.