El-CLASSICO: Dan Madrid ya kashe dan Barcelona a birnin Kano

0

Wani matashi a birnin Kano ya burma wa abokin sa wuka, jim kadan bayan tashi daga wasan da Real Madrid ta sha kashi da ci daya mai ban-haushi a hannun abokiyar adawarta, Barcelona.

Kisan ya faru ne ranar Asabar a lokacin da suka rukume gardama bayan tashi daga wasan, wanda suka kalla a cikin unguwar Yakasai, cikin birnin Kano.

An yi wasan ne ranar Asabar da dare, inda gardama ta rukume tsakanin Abdullahi Haruna da abokin sa Mujitapha Musa a kan wasan da suka rigaya suka kalla.

Ba a dai san takamaimen kalmomin da suka furta wa juna ba har Abdullahi ya burma wa abokin na sa Mujitafa wuka ba.

Baya ga kashe Mujitafa da ya yi, sai da Abdullahi ya ji wa wani mai suna Murtala Musa ciwo da wukar a guiwar sa.

Kakakin yada labaran ‘yan sanda na jihar Kano, ya shaida wa ‘yan jarida cewa an garzaya da Mujitafa da Murtala asibitin Murtala Mohammed da ke Kano, inda likita ya shaida musu cewa Mujitafa ya mutu.

Ya kara da cewa shi kuma Murtala ya na samun sauki a asibitin.

Kakakin ya ce tuni jami’an su sun cafke Abdullahi, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Share.

game da Author