SHEHU SANI: Majiyyacin da PRP ta kasa magance wa ciwo

0

Kamar Dino Melaye kamar Sanata Shehu Sani.
Wadannan sanatoci biyu a farkon shigar su Majalisar Dattawa kowa ya yi tsammani dama sai an rika hawa sama ana rikitowa kasa da su. Ba don komai ba kuwa, sai dama tun kafin su shiga takarar Sanata kowa ya san ‘yan taratsi ne a Najeriya.

Sani ya tari aradu biyu bayan shigar sa a majalisar dattawa. Aradu ta farko da ya dauka ita ce sukar wasu manufofi na Shugaba Muhammadu Buhari wadanda shi sanatan ke gani sun kauce daga turbar da aka san Buhari din ko kuma jam’iyyar APC sun ginu a kai.

Wannan ce ta haifar masa jangwangwama a Abuja, musamman daga bangaren uwar jam’iyya mai mulki, wato APC.

Aradu ta biyu da ya tara kuwa, wadda kusan ita ce ta zama tsawa ta fado masa a kai, har ta zama kwarankwatsar da ta kwararratse siyasar sa, shi ne fadan da ya rika yi da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya kasance sun raba hanya shi da El-Rufai, har sai da ta kai abin na su na neman zama gaba. Munin ya kai ga Sani ya shiga sahun wasu fitattun ‘yan APC da suka fice daga jam’iyyar suka koma PDP.
Sai dai kuma maimakon Sani ya shiga zugar masu komawa cikin PDP, sai ya lamfale, ya noke baya, daga bisani ya afka cikin jam’iyyar PRP.

A siyasar Najeriya, bambanci ko ratar da APC da PDP suka bai wa PRP, tamkar ratar fifiton kayan lodin tirela guda daya ne da kuma lodin jaki guda daya.

A irin wannan hali na jula-jula da karin kundumbalar siyasa, PRP ba zanin rufe katara ba ce. Duk da haka Sanata Sani ya dauke ta ya daura. Sai mayafin na PRP ya yi wa Sani abin nan da Hausawa ke cewa ‘baya ba zani’. Ko kuma kai tsaye a ce ya yafa zanin da bai iya rufe katara da shi.

Sani ya sha kaye a hannun dan gaban goshin El-Rufai, wato Uba Sani, wanda ya maye takarar sa a APC, bayan ya fice daga jam’iyyar.

Ko da ya ke Sanata Shehu Sani ya ce bai amince da zaben ba, domin ya ce abin da aka yi a zaben sanata a jihar Kaduna, ya zarce magudi, sai dai a kira shi da zamba, babu wanda zai iya cewa sanatan zai iya yin nasara a kotu ko a’a.

Share.

game da Author