Sani Sidi ya fice daga PDP, Yana shirin komawa APC tare da wasu jiga-jigan PDP a Kaduna

0

Tsohon shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, Sani Sidi ya sanar da ficewar sa daga Jam’iyyar PDP.

Sidi ya bayyana haka ne a wata takarda da tsohon Kakakin gwamnatin Kaduna, Ahmed Maiyaki ya saka wa hannu Inda ya ce gaba daya yadda Jam’iyyar PDP ke gudanar da ayyukanta a Kaduna ya saba wa manufofin Jam’iyyar da bisa dalilin haka ya sa dole su hakura da Jam’iyyar su Kama gaban su.

Sani Sidi na daga cikin ‘yan takarar da suka fafata a Zaben fidda gwanin gwamna na Jam’iyyar a watan Disamba.

Shine ya zo na uku a Zaben baya ga Isah Ashiru da ya lashe zaben da Sule Hunkuyi da ya zo na biyu.

Cikin wadanda suka fice daga PDP din tare da Sidi sun hada da, Rabiu Bako Peter Adada, Kabiru Balla, Sani Shahada, Kabiru Damau, Aliyu Ramin Kura, da Sadiq Hunkuyi. Bayannan akwai wasu kusan 30,000 Wanda Duk magoya bayan Sidi ne da suka mika takardar ficewa daga Jam’iyyar.

Idan ba a manta ba Ahmed Maiyaki ya tattara nasa-inasa ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC a wata sanarwa da ya mika wa manema Labarai a Kaduna ranar Asabar.

A sanarwar Maiyaki ya ce babban dalilin da ya sa ya fice daga PDP shine don rashin gamsuwar sa da zabin Isah Ashiru a matsayin Dan takarar gwamnan Jihar Kaduna.

” Idan za ka yi wa kanka adalci ba da irin dan takarar da PDP ta tsayar bane za a musanya goga irin El-Rufai a Kaduna. Nasir El-Rufai ya yi abin azo a gani da irin su Ashiru ba za su iya tabuka komai ba. A dalilin haka kuwa na ga ya fi dacewa mu mara wa El-Rufai baya domin ci gaban Jihar mu.

” Na dade in tattaunawa da neman shawara kafin na yanke wannan shawara. Babu wani dantakara a Kaduna da zai iya kwatanta irin ayyukan da El-Rufai yake yi a Jihar, wannan kowa ya gani Kuma ya shaida.

Maiyaki Wanda shine kakakin gwamnatin Kaduna a lokacin mulkin Ramalan Yero, ya mara wa Sani Sidi baya ne a Zaben fidda gwani na Jam’iyyar.

Akwai yiwuwar Sani Sidi da wasu daga cikin ‘yan Jam’iyyar PDP zasu biyo Maiyaki zuba Jam’iyyar APC din nan ba da dadewa ba.

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Kaduna, Umar Mohammed ya bayyana wa wakiliyar mu cewa sam ba su yi mamakin ficewar Maiyaki daga PDP ba.

” Dama can mun san da cewa zai Koma APC tun ba yanzu ba. Dama can yana tare da tsohon gwamna Ramalan Yero ne, amma ya juya Masa baya a Zaben fidda gwani na PDP ya koma yana yi wa Sani Sidi aiki. Bayan Ashiru ya naka su duka da kasa sai suka fara neman ficewa. Abinda nake so A sani shine itama APC zai fice idan yaji ba dadi.” Inji Umar.

Umar ya ci gaba da cewa, ko ficewar da Sani Sidi ma bai tadawa Jam’iyyar PDP da hankali ba, ” muna sane da cewa zai fice dama can. Duk alamu sun nuna. Tun bayan Kashi da ya Sha a Zaben fidda gwani muka San cewa akwai wata kullalliya. Umma-ta-gaida Aisha.

Share.

game da Author