Sanadiyyar bullowar cutar muran tsuntsaye a jihar Filato, wani likitan dabbobi, Spak Shaset ya bayyana cewa sun kashe kaji akalla 3900 a jihar a dalilin kamuwa da cutar.
Bincike ya nuna cewa wannan cuta na yawan bullowa ne a daidai lokacin da ake sanyi sannan mutum na iya kamuwa da wannan cutar idan an ci tsuntsu ko kuma kazar da ta kamu da wannan cutar.
Alamomin wannan cutar a jikin mutum sun hada da zazzabi, ciwon kai da mura sannan a jikin dabba kuwa mura da zazzabi ne.
” Bayan samun rahoton cewa cutar ta bullo a jihar Bauchi, sai muka yi kokarin ganin mun mun fara shirin yadda zamu kiyaye amma kuma bayan awowi 72 sai ga tabbacin bullowar wannan cuta a wasu gonaki dake kananan hukumomin JosTa Ta Arewa da ta Kudu inda a dalilin haka muka kashe kaji 3,900 nan take.
Shaset ya yi kira ga masu kiwon tsuntsaye da kaji a jihar da su rika yi wa kajin su allurar rigakafi da kuma tsaftace muhallin su.
Ya ce za a iya kashe duk tsuntsu ko kuma kazan da aka ga alamun wannan cuta a jikin sa sannan a birne gangan jikin domin hana yaduwar cutar.