Rundunar Sojin Sama ta kama barayin shanu 10, ta kwato dabbobi 57 a jihar Kaduna

0

Rundunar ‘453 Base Service Group’ na sojin sama ta kamo wasu barayin shanu guda 10 sannan ta kwato dabobbi 57 a jihar Kaduna.

Shugaban tawagar wadannan dakaru Idi Sani ya sanar da haka da yake hira da manema labarai ranar Talata a garin Kaduna.

Sani yace rundunar ta yi nasarar cafke wadannan bata gari ne a dalilin bin umurnin babbar hafsan sojin sama Sadiq Abubakar da ya bada na samar da tsaro musamman a wannan lokaci na zabe.

Dakarun sojojin sun yi arangama da wasu barayin dabbobi a dajin Riyawa. Sojojin suka fatattake su. Sun gudu sun bar Shanu 44 da raguna 13.

” A tsakanin ranakun 15 zuwa 16 ga watan Fabrairu dakarun sojojin sun kama wasu barayi 10 a kasuwar Amana, sansanin mahajjata dake Mondo da Mondo a Kaduna. Mun kama wadannan mutane da motoci biyu, bindigogi takwas,adduna takwas da wuka daya.

A karshe Sani ya ce rundunar za ta ci gaba da hada hannu da sauran jami’an tsaron dake jihar domin ganin an samar da tsaro a jihar.

Share.

game da Author