Harin Boko Haram ya hana Gwamna Geidam kada kuri’a

0

A dalilin hare- Haren Boko Haram da ya auku a garin Geidam, gwamnan jihar Yobe Ibrahim Geidam bai samu damar fita zuwa zabe ba.

Jami’an tsaro sun bayyana tuni dai har zaman lafiya ya dawo a garuruwan da Boko Haram suka kai wannan hari.

A yau ne garin Maiduguri ta tashi cikin rudani a safiyar ranar Zabe inda Bama-bamai har 11 suka tashi a garin.

Wani dan sanda ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES.

Bayan haka a wata majiyar kuma ta tabbatar cewa BokoHaram ta kai wa garin Gaidam dake jihar Yobe hari ranar Asabar.

Majiyar ta bayyana cewa Boko Haram sun kai wa garin hari ne da karfe uku na asuba.

Wata mazauniyyar garin Potiskum Fati Umar ta bayyana wa wakilin mu cewa tun daga wannan lokaci suka rika jin karan harsashin bindiga.

Bayan haka jiya da yamma wasu ‘yan kunan bakin wake na Boko Haram sun kai wa kauyen Zabarmari hari.

Kauyen Zabarmari kauye ce dake kusa da Jere da Maiduguri a jihar Barno.

Share.

game da Author