Buhari ya lashe mazabar Dankwambo a Gombe

0

A ci gaba da lallasa abokan takarar sa da ya ke yi musamman a jihohin Arewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a mazabar gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo.

Buhari ya samu ruwan kuri’u har 453 inda Atiku ya samu kuri’u 80 kacal.

Dankwambo da shima dan takarar kujerar sanata ne a jihar, ya lashe wannan mazaba inda ya doke abokin takarar sa na jam’iyyar APC, Saidu Ahmed Alkali, da kuri’u 325.

Share.

game da Author