An kama malamar da ta ci zarafin ‘yar shekara 4 a makaranta

0

Kotun majistare dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa wata malamar makaranta Adejuyigbe Moni hukuncin zama a kurkukun Kirikiri a dalilin cin zarafin wata ‘yar shekara 4 a makarantar.

Ita dai wannan malaman an kama da laifin cin zarafin wata ‘ya shekara 4 inda take cusa yatsarta a cikin gaban su.

Alkalin kotun Olufunke Sule-Amzat ta ce Moni za ta zaunan a Kirikiri ne har sai ta kammala yin shawara da fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka.

Dan sandan da ya shigar da karar mai suna Benson Emuerhi ya bayyana cewa Moni ta aikata hakane a ‘Covenant Tekno Kids Discovery Centre’ dake Igando a jihar Legas ranar 13 ga watan Janairu.

Ya ce sun gaggauta taso keyan Moni ne bayan mahaifin dalibar ya kawo kara ofishin su.

” Mahaifin yarinyar yace wata rana ‘yar su ta dawo gida tana kukan cewa gabanta na mata ciwo da mahaifiyarta ta tambayeta ne sai ta fadi mata cewa ay wata malama ce ta rika saka mata hannu a gaban ta a makaranta shine yasa yake mata zafi haka.

Sai dai kuma ita Moni ta musanta aikata haka.

Za a ci gaba da shari’ar ranar 11 ga watan Afrilu.

Share.

game da Author