RIKICIN KAJURU: El-Rufai ya yi ganawar sirri da shugaba Buhari a Abuja

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriyata ruwaito cewa gwamnan ya yi wannan ziyarar gaggawa ne domin yi wa Buhari bayanin abubuwan dake faruwa a jihar Kaduna game da rikicin garin Kajuru.

Babu wanda ke da masaniya game da abin da suka tattauna a wannan zama da suka yi duk da cewa zaman da suka yi bai gaza awa daya ba.

A safiyar Talata mutanen garin Maro suka tashi cikin tashin hankali inda wasu mahara suka far wa kauyen.

Wata ’yar asalin yankin mai suna Paulina Irimiya, ta ce an kai harin ne da misalin karfe 6:30 na safe.

Paulina wadda ke magana cikin firgici da kidimewa, ta yi zargin cewa Fulani ne suka kai musu harin.

Yankin Kajuru ya zama abin maida hankula kan sa tun bayan rikice-rikicen da suka rika faruwa a kai a kai, da ke haifar da mummunan kashe-kashe.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana kazamin harin da aka kai a rugagen Fulani cikin makonni biyu da suka gabata, cewa an kashe Fulani 130.
Harin da aka kashe Fulanin masu tarin yawa dai kabilun yankin ne su ka kai shi.

A yau Talata da safe kuma, Gwamna El-Rufai na Kaduna ya tabbatar da wannan sabon harin da aka kai.

Ya sanar da haka ne ta bakin kakakin yada labaran sa, Samuel Aruwan.

Sanarwar ta ce wannan sabon harin ya fantsama har cikin Karamar Hukumar Kachia, wadda ke makautaka da Kajuru.

Gwamnan ya tabbatar wa jama’a cewa jami’ann tsaro nab akin kokarin su wajen ganin sunn shawo kan rikicin.

“Gwamnati da damu kwarai da wannan sabon hari, ta yi Allah-wadai da shi, kuma ta na kira ga jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro wajen kare lafiyar al’ummar yankin.”

Share.

game da Author