Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe zaben 2019 na shugaban kasa da kuri’u milyan 15,191,847. Ya yi nasara a kan abokin karawar sa na PDP, Atiku Abubakar.
Atiku wanda ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007, ya samu kuri’u 11,262,978.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC , Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana sakamakon zaben, bayan shafe kusan kwanaki biyu ana bayyana sakamakon zabe.
GA JAWABIN BAYYANA SAKAMAKO
“Ni Farfesa Mahmood Yakubu, ina tabbatar da cewa ni ne Babban Jami’in Bayyana Sakamakon Zabe na Kasa da aka gudanar a ranar 23 Ga Fabrairu, 2019.
“Kasancewa Muhammadu Buhari ya cika sharuddan da doka ta tanadar na samun kuri’u mafi rinjaye, ya yi nasarar komawa kan kujerar sa sakamakon sake zaben sa da aka yi.”
Yakubu yace INEC za ta mika wa Buhari takardar shaidar sake lashe zabe a yau Laraba, karfe 2 na rana.