Fitacce kuma kwararren dan wasan kasar Masar da ke buga wa kungiyar Liverpool da ke Ingila, Mohammed Salah, ya sake lashe kambun Gwarzon Dan Kwallon Afrika na shekarar 2018.
Ko a shekarar da ta gabata shi ne dai ya lashe gasar ta 2017.
Ita kuma ‘yar Najeriya da ke rike da kambun Gwarzuwar Mata, Asisat Oshoala, a wannan karon an kwace kambun daga hannun ta.
Salah, dan shekara 26, shi ne dan kasar Masar na farko da ya taba lashe gasar tun farkon shigo da ita, cikin 1992.
Thembi Kgatlana ce ta lashe gasar a bangaren gwarzayen ‘yan kwallo mata na Afrika.
Oshoala ‘yar Najeriya ta zo ta biyu, bayan ta taba samun nasara har sau uku a 2014, 2016 da kuma 2017.
An gudanar da bikin bada kyautukan a Dakar, Babban Birnin kasar Sanagal.
A wannan shekarar babu dan Najeriya ko daya a cikin wadanda suka gwabza neman zama zakaran Afrika a bangaren maza.
Discussion about this post