Buhari ya sake dora laifin matsalar tsaro a kan Gaddafi

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nanata cewa mukarraban tsohon shugaban Libya, Mu’ammar Gaddafi ne suka haddasa barkowar matsalar ta’addanci a Najeriya.

Ya ce masu bindigar da suka tsere daga Libya, bayan kashe Gaddafi a cikin 2011, sun koma aikata ta’addanci, bala’in da ya ce ke ta addabar Najeriya da wasu kasashen Afrika.

Buhari ya fadi haka a hirar da Mujallar Arise da jaridar THISDAY ke bugawa.

Gaddafi wanda ya shugabanci kasar Libya a tsaron lokaci, an kashe shi ne cikin 2011 a yayin guguwar neman sauyin da ta tirnike wasu kasashen Larabawa, inda mutane suka rika kafa kungiyoyin tawaye suka yakar shugabannin su.

Ba kamar yadda wasu ke ganin cewa kashe-kashe a kasar nan aikin ta’addancin cikin gida ne, shi kuma Buhari ya yarda da cewa sakamakon rikicin Gaddafi ne abin ke ta bibiyar Najeriya.

“Gaddafi ya shafe shekaru 43 ya na mulki, har ta kai shi ga tunanin daukar nauyin matasa a kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Najeriya, Chad da Afrika ta Tsakiya ana koya musu yadda za su rika kashe mutane.

“To lokacin da ‘yan tawaye suka kashe Gaddafi, sai suka gama da wasun su, wasu kuma suka tsere. To wasun su sun gudo har nan cikin Arewacin Najeriya, inda har yanzu mu ke ta fama da su a Arewa maso Gabas su na kai hare-hare.’n Inji Buhari.

Ba wannan ne karo na farko da Buhari ya dora laifin a kan Gaddafi ba.

Share.

game da Author