Sama da ’yan takara 20,000 za su shiga zaben 2019 – INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce sama da ‘yan takarar mukamai daban-daban za su shiga zaben 2019 da za a gudanar cikin watan Fabrairu da Maris.

Hukumar ta ce ba a taba samun yawan ‘yan takara a tarihin zaben Najeriya ba kamar zaben 2019 mai zuwa.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, a jiya Talata lokacin da ya ke ganawa kafafen yada labarai a hedikwatar INEC, a Abuja.

Ya ce ba a taba samun wannan adadin ba a dukkan zabukan da aka taba gudanarwa a baya.

Ya ce cikin wannan satin ne za a kididdige yawan wadanda ke takarar mukamai daban-daban a Babban Birnin Tarayya Abuja da kewayen ta.

Yakubu ya ce akwai masu takarar sanata har 1,800, masu takarar majalisar tarayya su 2.600.

Ya ce akwai kujerun majalisar jihohi har 991, wadanda ‘yan takara 14,000 kowa kenan samun nasara.

Yakubu ya ce za a gudanar da zaben har wurare 120,000.

Share.

game da Author