2019: Fitacciyar ‘Yar jarida Kadaria Ahmed zata jagoranci taron tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasa

0

Fitacciyar ‘Yar Jarida Kadaria Ahmad ta shirya taron ganawa da tattaunawa da ‘yan takarar shugaban kasar nan inda za su bayyana gaban jama’a su tattatauna batun kasar nan da shirin da suke wa kasa Najeriya idan suka yi nasara a zabe mai zuwa.

Kadaria ta shirya wannan taro ne da ta yi wa suna ‘Yan Takara’ domin mutanen Najeriya su samu daman ganawa da ‘yan takarar su sannan su iya yi musu tambayoyi game da kasa Najeriya da irin shirin da kowa yayi wa kasar idan ya samu nasara a zabe mai zuwa.

Ana sa ran ‘yan takarar hudu ne tare da mataimakan su za su bayyana a wannan wuri da za a gudanar da wannan taro.

Kamar yadda shirin yake, za a fara ne da dantakarar shugaban kasa na jam’iyyar YYP, Kingsley Moghalu da mataimakiyar sa Umma Getso ranar 9 ga watan Janairu.

Bayan nan ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo na jam’iyyar APC zasu bayyana a wajen taron domin tattaunawa da mutane da amsa tambayoyi daga zababbun wadanda suka halarta.

Buhari da Osinbajo za su bayyana a ranar 16 ga watan Janairu.

Ranar 23 ga watan Janairu kuma dan takara na jam’iyyar AACP, Omoyele Sowore da mataimakin sa Rabiu Rufai zasu bayyana.

Daga nan kuma sai dan takara na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da mataimakin sa Peter Obi su bayyana ranar 30 ga watan Janairu.

Kadaria ta ce za a nuna wannan taro da tattaunawa kai tsaye a tashoshen Talabijin na Kasa, NTA da wasu da kuma gidan radiyon tarayya FRCN.

Za a iya bin shirin kai tsaye ta shafin www.daria.com a yanar gizo

Share.

game da Author