Wata kwallo da dan wasan Real Madrid, Casemero ya zandama daga nesa a ragar kungiyar Sevilla, ta sa ‘yan kallo magoya bayan Madrid sun daina jin sanyin da ke fama da shi a birnin Madrid.
Kwallon ta zo ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, yayin da har ana tunanin canjaras za a tashi wasan.
An kusa tashi ne kuma fitaccen dan wasa Luka Modric ya kara sheka wa Sevilla kwallo daya a raga.
Magoya baya sun tafi gida suna murna, ba tare da karkawar sanyin da ake fama da shi a kasar ba.
Casemero ya ci kwallon sa ce ana saura minti 12 a tashi wasa, yayin da shi kuma Modric ya jefa tasa ana kusa da hura tashi.
Sevillla sun yi sakaci ne daga karshen wasan, saboda sun koma tsare gida, inda suka bar mai tsaron gidan su da faman aiki, har daga karshe aka yi musu aika-aika.