Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, Atiku Abubakar, ya dawo daga ziyarar gayyata ta kwanaki biyu da ya kai Amurka.
Ofishin dan takarar ya ce Atiku ya iso filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja da karfe 3:15 na rana, inda magoya baya suka tare shi.
Ya yi ganawa ce da jami’an majalisar Amurka da kuma manyan ‘yan kasuwa masu zuba jari.
Ya je Amurka ne tare da Daraktan Kamfen din sa, Bukola Saraki.
Dawowar Atiku ta kashe bakin tsanyar masu cewa bai isa ya je Amurka ba, da kuma masu cewa bai isa ya je ya dawo ba.
Dawowar sa ke da wuya sai ya garzaya dakin da ke gudanar da muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa.
Da ya isa wannan dakin taro sai ya fahimci cewa shugaba Buhari ba zai halarta ba, daga nan ne ya ce ba zai zauna a wannan wuri ba.
” Ba zan tsaya ina ta surutu ba, bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai halarta ba. Shine yaka mata in fafata da.”
Daga nan sai karkada ya yi tafiyar sa.
Discussion about this post