2-0: Yadda mai tsaron bayan Arsenal, Koscielyn ya kafa tarihi a kan Chelsea

0

Wasan Premier na yau da aka buga tsakanin kungiyar Arsenal da Chelsea, su biyun da ke birnin Landan, ya tashi da ci 2:0 a kan Chelsea.

Chelsea ta sha kashi ne a wasan, wanda mai tsaron bayan Arsenal, Laurent Koschielyn ya aje muhimmin tarihi bayan ya jefa kwallo a ragar Chelsea.

Shi ne dan wasa mai tsaron baya na farko da ya taba ko ya fara cin kwallaye 20 a gasar Premier.

Ya fara wasa a Arsenal tun 2010, kuma ya jera kakar wasa 9 kenan babu wadda bai ci kwallo ba.

A tarihin gasar ba a taba samun dan wasa mai tsaron baya da ya ci kwallaye 20 ba, sai shi.

Laurent ya na buga wa kasar Faransa wasa ne kuma.

Share.

game da Author