Yadda hatsarin mota ya ritsa da tsohon gwamna Fayose a Legas

0

Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya hadu da hatsarin mota, a kan doguwar gadar nan ta ‘Third Mainland Bridge’ dake Lagos.

An ce kiris ya rage hadarin ya kashe Fayose, wanda kakakin yada labaran sa, Lere Olayinka ya bada labarin faruwar sa a shafin sa na tiwita.

Sai dai bai yi wani dogon bayani ba. Amma dai ya ce hatsarin ya faru ne jiya Laraba da rana a kan gada.

Amma dai ya ce ya na samun sauki sosai, domin likitoci da jami’an jinya na bas hi kulawa matuka.

Da ya ke yin karin haske a shafin sa na tiwita, Olayinka ya ce Fayose na kara samun sauki sosai.

“Ina farin cikin shaida muku cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya samu sauki sosai.”

“Fayose ya kara gode wa Allah da ya takaita munin hatsarin, musamman ma a kan sauran wadanda ke cikin motar.”

Olayinka ya ce duk da wannan hatsari da ya faru, tuni Fayose har ya garzaya garin Ibadan domin halartar taron kamfen na dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Fayose ne kodinatan kamfen na Atiku a yankin Kudu Maso Yamma.

Ya ce Fayose na nan a kan jajircewar sa domin ganin PDP ta kafa gwamnati a zaben 2019.

Share.

game da Author