BADAKALAR GANDUJE: Kotu ta dakatar da majalisar Kano binciken Ganduje kwata-kwata

0

Mai shari’a Ahmad Badamasi na babbar kotu dake jihar Kano ya yanke hukuncin dakatar da majalisar jihar Kano daga ci gaba da bincikar badakalar karbar cin hancin dala miliyan 5 da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya rika karba daga hannun ‘yan kwangila.

Idan ba’a manta ba Jaridar Daily Nigerian ta bankado badakalar karbar cin hanci da ya nuna gwamna Ganduje kuru-kuru yana karkacewa yana zura bandir-bandir din daloli na cin hanci daga hannun wani dan kwangila a aljihun jamfar shakwarar sa.

Majalisar jihar Kano ta gayyaci mawallafin wannan jarida, Ja’afar Ja’afar da ya bayyana a gaban ta domin yayi mata bayani game da wannan bidiyo da ya wallafa.

Sai dai kuma bayan haka aka shigar da kara kotu kan a dakatar da majalisar daga ci gaba da bincikar wannan badakala na gwamna Ganduje inda a kwanakin baya kotu ta umarci majalisar ta dakatar da haka har sai an yanke hukunci a kan haka.

A yau Alhamis, kotu ta yanke hukuncin dakatar da majalisar kwata-kwata daga ci gaba da bincikar gwamna Ganduje cewa wannan ba a hurumin majalisar ya ke ba.

A hukuncin da maishari’a Badamasi ya yanke, ya ce majalisar ba ta da ikon bincikar abin da ya shafi cin hanci da rashawa. Ya ce wannan yana hurumin hukumomin ICPC ne da EFCC.

Sannan kuma ya hana majalisar da kada ta kuskura ta sake kiran wani ya bayyana a gabanta bisa ga wannan magana.

Lauyan majalisar Kano, Mahmud Waziri, ya bayyana cewa ba shi da abin da zai fadi yanzu sai abin da majalisa ta yanke. Idan zata daukaka kara shi a shirye yake.

Shi ko shugaban kwamitin Bappa Dan’ agundi, cewa yayi majalisar za ta bi hukuncin shari’ar daki-daki shari’ar sannan ta bayyana matsayin ta nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author