Yawan Mutuwar Aure a Kasar Hausa, Daga Dr Usman Abubakar

0

Yana da kyau mu fara fahimtar menene aure. Aure ibada ce, a inda mace da namiji suke yadda su zauna tare domin su gudanar da rayuwarsu cikin zaman lafiya da annashuwa. Anayin aure ne domin a hayayyafa, a kuma raya sunnar Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wa Sallam. Saboda Annabin mu yana cewa “kuyi aure ku hayayyafa, domin inyi alfahari daku gobe kiyama”.

Shin menene yake kawo yawan mutuwar aure a kasar hausa?

Akwai abubuwa masu yawan gaske wadanda suke jawo sanadiyar mutuwar aure. Kadan daga cikinsu, suna abkuwa ne tun kafin ayi auren, wadansu kuwa suna faruwa bayan ma’auratan suna zaune tare.

Wadanda suke abkuwa kafin auren sun hada da rashin sanin ilmin aure, soyayyar karya da son abin duniya. A lokuta da dama soyayyar karya na gudana tsakanin namiji da mace, a inda daya daga cikinsu, baya son guda, amma sai yake/take nuna soyayyar karya. A irin wannan yana yin idan anyi auren, to ba zai dauki lokaci mai tsawo ba zai mutu, saboda tun farko an daura shine a bias sigar karya.

Abu na uku da yake haddasa mutuwar aure, tun ma kafin ayi auren shine yawan son abin duniya daga mazan da matan. Misali sai kaga namiji yana furtawa wai shi ba zai auri yarinya ‘yar gidan Malam Shehu ba, (watau talaka). Shi yafi son ya auri ‘yar gidan attajiri (watau mai kudi) wanda zai basu gida su zauna, da mota da kuma gwaggwabar gara, wacce zasu dade suna amfani da ita.

Daga bangaren matan kuma, suma akwai wadanda mai abun hannun (kudi) kawai suke so su aura. A inda zaka ji suna cewa su sai hadadden gaye kawai zasu aura. Watau wanda yake ta tabkeken gida, da manyan motoci da kudi a makare a banki.

Don haka a inda aka yi aure a bisa wannan tafarkin, to shima baya dadewa ma’auratan zasu fara samun matsala, saboda anyi auren ne kawai saboda son abin duniya. Ba wai soyayyar Allah da Annabi ba.

Abubawan dake kawo mutuwar aure bayan an daura shin a samuwa ne ta bangare biyu. Watau ta hanayar mata ko miji.

Ta bangaren mata sun hada da; kazanta, rashin iya girki, rashin gama abinci akan lokaci, da almubazanci. Sauran sun hada da rashin lafazi mai kyau/dadi ga mai gida, yawan fada da mutane ko dangin miji, yawan fita unguwa babu izni, yawan tambayar miji kudi, cin bashin mutane ba tare da izinin miji ba, da rashin ladabi ga miji, rage kudin cefane da zubin kudin adashi da su da sauransu.

Ta bangaren maza, abubuwan dake sanadiyar mutuwar aure sun hada da; rashin nuna kulawa da kwalliyar mata, da iya girkinta, tsafta, da sauran harkokinta nay au da kullum. Sauran abubuwa sun hada da rashin sayamata kayan kwalliya da gyara jiki, yawan yi mata fad aba tare da binciken laifin da aka yi ba, yawan hantara da zagi.

Bugu da kari, akwai rashin fadar gaskiya a harkar zaman tare, da yawan kula mata, da rashin zaman gida tare da mu’amala da iyali. Abu na karshe da yafi ciwa mata tuwo a kwarya shine yawan amfani da waya a kodayaushe a cikin gida. Watau suna ganin cewa maza basu da lokacinn kula su a cikin gida, sai dai suyi ta danne-dannen wayar su.

Kadan daga cikin illolin da mutuwar aure ke haifarwa ta hada da yawan zawarawa, ‘ya’yan da aka bari a gidan mahaifinsu, basa samun kulawa, sai ma tsangwama da suke samu daga matar da mahaifinsu ke aura daga baya. Yaran kuma sukan tashi a cikin damuwa, wanda yakansa su rashin kokari da hazaka a makaranta.

Hanyoyin da za’abi ayi maganin yawan mutuwar aure a kasar Hausa sun hada da; gina aure a doron soyayyar gaskiya, rage son abin duniya, sanin ilimin auren kafin ayi shi. Sauran sun hada da iyaye su koyawa ‘ya’yansu mata tsafta, girki da ladabi da biyayya kafin aurar dasu.

Mazaje su rinka ba wa matayensu kulawa ta musamman, da kuma yaba masu idan sunyi girki mai dadi ko kuma kwalliyar data burgesu. Sannan su kuma yi kokari suna zama tare da iyalensu a cikin gida. Har ila yau su daina amfani da wayarsu idan suna tare da iyalensu, sai dai idan kiransu akai a wayar to sai su amsa.

Talauci na daya daga cikin abubuwan da suke sa mutuwar aure a kasar Hausa domin zaka saurayi daya sami ‘yan kudin sa bai da wata sanar yi sai kaji yace shi aure zai yi batare da iyayensa sun nusar dashi ga yadda aure yake ba. Daga zarar anyi auren yau da gobe kuma sun cinye dan kayan da aka kawo masa, ya buga nan ya buga can babu sai kaga hankali ya tashi daga an taba shi sai kaji fada daga nan sai rigima, kafin kace wani abu sai rikici ya tashi daga nan sai saki.

Wasu lokuta kuma iyaye mata sukan bada gudunmowa wajen mutuwar aure, wannan ya biyo bayan za ka ga iyaye mata na sanya ‘ya’yayen su mata da yawan fita zuwa biki, suna, gaisuwa da makamantan irin wadannan abubuwa. Idan maigida ya dauki matakin hanawa sai ace zai raba matarsa da dangi, idan kuma ya zama sakwa-sakwa sai tarbiyar yaransa data matarsa ta lalace. Domin ta wannan hanyar zata gano wani abu ga wata mata kuma mijinta bai kai karfin yayi mata wannan abu ba amma sai ta tilasta da cewar ita ma sai yayi mata haka.

Sannan kishi yana kasha aure yasa yawan zawarawa ta hanayar kishi, idan matar mutum mai kishi ce bata son taji yace mata zai yi mata kishiya, kai ko da wasa akayi mata maganar kishiya sai kaga ta tashi hankalinta. Ta shiga malamai da boyakaye wai ita dai kada mijinta yayi mata kishiya, bashin Allah ya wajabtawa namiji da cewar ya auri mataye hudu, to amma sai kaga mace tayi biris da wannan batu su kuma tubure cewar basu yarda ba wannan lamari.

Auren da aka ginashi akan kwadayi ko yaudara ta nuna karya, ko kuma kwadayi a yayin da gaskiya ta tabbata sai kaga rikici ya balle har ka rasa ta yaya akai wannan aure domin rikici mai zafi zai faru har kuma kaga igiyar aure ta mutu cikin kankanen lokaci.

Wasu kuma sukanyi sihiri wajen yin aure ta fuskar shiga bokaye da malamai saboda mahaukaciyar soyayyar dayansu, lokacin da shirin ya karye sai kaga damuwa ta bullo daga nan sai mutuwar aure domin ba ayi auren akan turbar soyayyar gaskiya ba.

Daga Dr Usman Ibrahim Abubakar, Bayero University Kano

Share.

game da Author