An zargi ma’aikatan Hukumar Kasashen Afrika da yin lalata da mata masu neman aiki

0

An zargi wasu ma’aikatan Hukumar Kasashen Afrika da neman rika yin lalata da ma’aikatan da aka tura musu domin yin ayyuka na wucin’gadi.

Wani rahoton cikin gida na kungiyar ne ya tabbatar da faruwar haka a kan mata matasa da ke zuwa ko dai gudanar da ayyukan sa-kai, ko kuma ayyuka na wucin-gadi.

Kamar yadda Gidan Radiyon BBC ya ruwaito, wannan kokarin tirsasa mata a yi lalata da su babbar matsala ce ga masu aiki da masu neman aiki a Kungiyar Kasashen Afrika.

Rahoton ya ce abin bakin ciki kuma shi ne, masu aikata wannan badalar su ne manyan masu kula da ofisoshin kungiyar ko hukumar.

BBC ta yi wannan rahoto ne bayan samun kwafen wata wasika da aka aika wa shugaban hukumar, Mousa Faki, inda aka sanar da shi bahallatsar da ke gudana a hukumar ta AUC.

An samu rahotanni har 44 da suka tabbatar da yadda ake lalata da wasu matan da kuma yadda sai an yi lalata da wasu kafin a dauke su aiki.

Duk da dai ba a bayyana sunayen wadanda ake zargi ba, amma dai rahoton ya nuna cewa wadanda ke aikata bahallatsar, su na yi wa ‘yan matan alkawarin idan suka ba su hadin kai, to za su samar musu aiki ko kwangila ba tare da samun wani cikas ba.

An kuma gano cewa wasu mata 37 sun rubuta wasikun korafin neman yin lalata da su, wanda hakan shi ma ya kara haifar da gaggauta binciken da aka gudanar.

Share.

game da Author