‘Yan Najeriya na kashe naira tiriliyan 1 kowace shekara wajen tafiya karatu kasashen waje – Tsohon Shugaban Jami’a

0

Shugaban Jami’ar Crawford, kuma tsohon Shugaban Jami’ar Lagos, Farfesa Oye Ibidapo-Obe, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na kashe akalla naira tiriliyan 1 duk shekara wajen tafiya karatun digiri kasashen waje.

Farfesan ya fadi haka ne jiya Laraba, a lokacin da ya ke jawabi a bikin yaye dalibai karo na 10 na Jami’ar Crawford da ke garin Igbesa, jihar Ogun.

Ya fallasa yadda ake kashe wadannan makudan kudade ne, daidai lokacin da majalam jami’o’in Najeriya ke ci gaba da gudanar da yajin aikin da suka fara tun daga ranar 4 Ga Nuwamba.

Daga nan ya ci gaba da nuna muhimmancin ci gaba da kafa jami’ao’i masu zaman kan su wadanda ba na gwamnati ba Najeriya.

Ya ce ta haka ne za su kara samun ingancin da za a rage karakainar neman karin ilmi a kasashen duniya, inda ake kwasar makudan kudade ana tafiya da sunan tafiya karin ilmi.

Share.

game da Author