2019: INEC ta bayyana matakan gudanar da zabe a sansanonin masu gudun hijira

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana wasu hanyoyi da matakan da za a bi, domin ganin cewa dukkan wadanda suka yi rajista, amma suke a sansanonin gudun hijira fadin kasar nan baki daya sun jefa kuri’a a zaben 2019.

Shugaban Hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka, cewa akwai dimbin masu zaune a sansanonin gudun hijira, sakamakon hare-haren Boko Haram, fadace-fadacen makiyaya da manoma da sauran fadace-fadacen kabilanci.

Yakubu ya ce akwai matukar ganin cewa ba a tauye musu ‘yancin su na yin zaben 2019 ba.

A taron Yakubu ya fitar da wasu matakai da hanyoyi a gaban wakilan kungiyoyi da dama, irin su USAID, UKAID da IFE a jiya Laraba.

An raba sansanonin gudun hijira gida biyu da suka hada da:

WADANDA KE ZAMAN GUDUN HIJIRA A JIHAR SU

Wadannan su ne wadanda rikici ya kora su ke zaune a cikin sansanin gudun hijira a cikin jihar da suke, inda suka yi rajistar zabe.

Shugaban Kwamitin Zabe a kan masu gudun hijira, Okechukwu Ibeano, ya ce wadanda ke zaman gudun hijira a jihar su za su jefa kuri’a a dukkanin zabukan da za a gudanar na 2019.

WADANDA KE ZAMAN GUDUN HIJIRA A JIHOHIN DA BA NA SU BA

Su kuma wadanda ke zaman gudun hijira a jihohin da ba na su ba, kuma ba a can suka yi rajista ba, za su yi zaben shugaban kasa ne kadai. Domin haka zai kawar da zargin da wahallalun daukar sakamakon zabe daga wannan kan iyakar jiha zuwa waccan.

Ya kara da cewa su rumfunan zaben cikin sansanin masu gudun hijira, za su kasance takardun bayyana sakamakon su daban suke da sauran na mazabu.

Daga nan sai ya kara da cewa za a yi amfani da tsarin shelanta wa masu gudun hijira yadda komai ya ke dalla-dalla tare da wayar musu da kai ta hanyar amfani da yare ko harshen su da suka fi fahimta a sansanonin masu gudun hijira.

Share.

game da Author