Babban Jami’in Soja mai kula da ‘Opereation Safe Corridor’, Manjo Janar Bamidele Shafa, ya bayyana cewa za a sako wasu watu tubabbun ‘yan Boko Haram 154 su dawo cikin jama’a.
Shafa yace tubabbun wadanda aka yi wa girkar kakkabe akidar ta’addanci a zukatan su, a yanzu sun zama nagari, sun yi watsi da waccan akida ta Boko Haram.
Ya yi wannan jawabi ne a Gombe a wurin ranar yaye su daga shirin yi musu girkar cire akidar ta’addanci a zukatan su, a garin Gombe.
Ya ce an ma rigaya an yaye wasu a baya, wadannan su ne kashi na biyu da aka yaye tun bayan fara aiwatar da shirin.
‘Kashi na farko su 95 ne, kuma an sallame su tun cikin watan Fabrairu, inda yanzu haka su na cikin al’umma kowa ya kama harkar gaban sa.” Inji Bamidele.
“Su ma wadannan su 155 din da iznin Allah mun kawo ranar da za mu sallame su, mu mika su ga gwamnatocin jihohin su, domin a samar musu madogara a cikin al’umma.”
Da ya ke magana a wurin taron, kwamandan gyaran halaye da dabi’un tubabbun Boko Haram, Kanar Beyidi Martins, ya ce ana samun tallafi da ga Amurka da wasu kasashen Turai.
Daga nan sai ya ce an koya wa tubabbun sana’o’in hannu iri daban-daban, wadda idan suka koma cikin al’umma za su iya yi domin su dauki dawainiyar rayuwar su ta yau da kullum.