Buhari ya nada Kabiru jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Kabiru Bala sabon jakadan Najeriya a Kasar Afrika ta Kudu.

A sanarwar haka da ya fito daga ofishin ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama, kakakin ministan Sarah Sanda ta bayyana cewa tuni har an mika wa Kabiru takardar fara aiki.

Kafin nadin nasa, Kabiru ne mataimakin jakadan Najeriya a kasar Britaniya.

Idan ba a manta ba, jakadan kasar Afrika ta kudu kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja, Musa Ibeto ya ajiye aiki don yin takarar gwamnan jihar Neja a jam’iyyar PDP.

Tun a zaben fidda gwani a ka wancakalar da shi.

Share.

game da Author