Sanatocin da suka ‘ci taliyar karshe’

0

Akwai Sanatoci da dama wadanda sun yi iyakar kokarin ganin sun sake komawa a majalisar Dattawa a zaben 2019, amma sun sha kaye a zaben fidda-gwani.

Wadanda da wahalar gaske su koma majalisa, sun kusa 40, amma mai yiwuwa kadan daga cikin su sa iya maye gurbin wasu nan da 17 Ga Nuwamba, idan jam’iyyar da suke ciki ta yi canjin sunayen wasu ‘yan takara daga hannun INEC.

Ga sunayen sanatocin da suka yi adabo da Majalisar Dattawa:

Adamawa

Abdulaziz Nyako (APC Adamawa ta Tsakiya) da Ahmed Abubakar (APC, Adamawa ta Kudu).

Bayelsa

Dukkan Sanatocin Bayelsa uku, Forster Ogola, Ben Murray Bruce da Emmanuel Paulker ba za su koma majalisar dattawa ba. Forster Ogola ya fadi zaben fidda gwani, yayin da Kwamishinan Ayyukan Jihar Bayelsa ya kayar da shi, Bruce ya ce ya gaji haka nan, ba zai koma ba.

Benue

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, wanda tun 1999 ya ke wakilci a majalisar Dattawa, ya sha kaye a zaben fidda-gwani.

Borno

Sanatocin Barno guda biyu, Baba Kaka Garbai da Abubakar Kyari duk ba za su koma ba. Garbai kayar da shi aka yi a zaben fidda-gwani, shi kuma Kyari ya janye, ya bar wa Kwamishina Umara Zulum.

Cross River

John Enoh (APC, Cross Rivers ta Tsakiya) shi ne dan takarar jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar a 2019, don haka ba zai koma majalisa a 2019 ba.

Ebonyi

Sonny Ogbuoji (APC, Ebonyi ta Kudu) a yanzu shi ne dan takarar gwamna a APC, don haka ko da ya fadi zaben gwamna, ba zai koma majalisar dattawa ba.

Enugu

Gilbert Nnaji (PDP, Enugu ta Gabas) ya sha kayae a zaben fidda-gwani, a hannun tsohon gwamna Chimaroke Inamani. Don haka ba zai koma majalisa ba.

Ekiti
Fatima Raji Rasaki ba za ta koma majalisa ba, saboda ta rasa kujerar tun a zaben fidda-gwani.

Gombe

Usman Nafada and Joshua Lidani ba za su koma ba. Nafada shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Gombe, shi kuma Lidani ya sha kaye ne a hannun mace, Binta Bello, wacce a yanzu ‘yar majalisar tarayya ce.

Imo

Hope Uzodinma (APC, Imo ya Arewa) ba zai koma ba, saboda shi ne dan takarar gwamna a jam’iyyar APC. Ya kayar da sirikin Gwamna Rochas Okorocha, Uche Nwosu. Amma dai har yanzu ta na kasa ta na dabo.

Shi ma Sanata Sam Anyanwu, ba zai koma ba, saboda ya sha kaye a hannun Emeka Ihedioha a karkashin jam’iyyar PDP.

Katsina

Abu Ibrahim da Umar Kurfi duk ba za su koma majalisa ba. Sanata Abu ya yanke shawarar kin sake tsayawa takara ne, shi kuma Kurfi ya sha kaye a hannun Kabir Barkiya a zaben APC na fidda-gwanin Katsina ta Tsakiya.

Kwara
Rafiu Ibrahim da Shaaba Lafiagi duk ba za su koma majalisar dattawa ba.

Mr Ibrahim Ibrahim ya sauka ne domin gwamna Abdulfatah Ahmed shi ma ya dana kujerar. Shi kuma Lafiagi karambani ya sa ya tsaya takarar gwamna a karkashin PDP, amma tun a zaben fidda-gwani aka baras da shi.

Lagos

Gbenga Ashafa ya sha kayen bazata a hannun dan majalisar jiha, Bayo Osinowo.

Nasarawa

Aruwa Gyunka (PDP, Nasarawa ta Tsakiya) ya ci kasa a zaben fidda-gwani, ba zai koma majalisa ba.

Niger
Sabi Aliyu Abdullahi da David Umaru duk sun sha kaye a zaben fidda-gwani, sun yi adabo da majalisa a 2019.

Ogun
Dukkan sanatocin jihar Ogun ba za su koma ba. An maye gurbin Buruji Kashamu da Bola Kalejaiye, shi kuma Sanata Lanre Tejuoso da Gbolahan Dada an maye gurbin su da Gwamna Ibekunle Amosun da Tolu Odeboyi.

Osun
Sanatocin Oshun uku duk ba za su koma majalisa ba. Olusola Adeyeye na APC da Babajide Omoworare na APC sun sha kaye a zaben fidda gwani. Shi kuma Ademola Adeleke ya tsaya takarar gwamna ne, kuma bai yi nasara ba.

Oyo
Rilwan Akanbi ya sha kaye a zaben fidda-gwani.

Filato
Joshua Dariye da Jeremiah Oseni ba za su koma ba.

Dariye ya na fuskantar daurin shekaru 14v a gidan kurkuku, shi kuma Useni shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Filato.

Rivers
Sanata Magnus Abe na APC ya fadi zabe, amma magana ta na kotu.

Yobe
Bukar Abba Ibrahim ba zai koma ba, saboda gwamna Geidam ya maye takarar sa.

Zamfara
INEC ta ce ba a yi zaben fidda gwani a Zamfara ba, don haka babu takarar APC a zaben 2019 a jihar. Dama kuma dukkan sanatocin jihar ‘yan APC ne.

Share.

game da Author