Takardun makaranta na garau suke babu karya a cikin su – Isah Ashiru

0

Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a inuwar jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya karyata rade-radin da ake ta yada wai takardun makarantar sa duk na boge ne.

Ashiru ya bayyana haka ne a takarda da ofishin yada labaran sa ta fitar, wanda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ashiru ya hori magoya bayan sa da su yi watsi da wannan zantuka cewa jam’iyyar APC ce ke shirya masa wannan tuggu don ta bata shi a idanun mutanen jihar Kaduna.

” Ina za a ce wai takardun makaranta na na boge ne bayan sau hudu ina takara a kasar nan kuma da su wadannan takardu nayi wadannan takara.

Ashiru ya ce irin wannan bita da kullin da ake masa ba zai sa ya yi faduwar gaba ba yana mai cewa yana nan daram kuma ya fito da karfin sa don kada jam’iyyar APC a zabe mai zuwa a jihar.

Share.

game da Author